Sanar wa mai muhimmanci: Bayani akan Kudin Jarabawa

·

·

Assalamu Alaikum Iyaye da Masu kula da yara.

Da fatan kuna cikin ƙoshin lafiya.

Mun rubuto muku ne domin sanar daku halin da ake ciki da matsaya da muka ɗauka kan batun abinda ya shafi jarabawar Yara.

Kowa yasan halin da ake ciki na tsadan kayayyaki a wannan lokaci da muke ciki. Hakan yasa Kayayyaki da muke amfani dasu na wurin gudanar da jarabawa sun ƙara kuɗi ta yadda gudanar da jarabawar yadda muka kasance mukeyi a baya abune wanda makaranta bazata iya ɗaukan nauyin sa ita kaɗai ba.

Saboda haka ne mukayi zama da Board na PTA wanda suke wakiltan ku domin samun mafita kan wannan lamari. Bayan tattaunawa da shawarwari mun samu matsaya kamar haka.

  • Kowani ɗalibi zai biya Naira 200 na Kuɗin Jarabawa.
  • Za’a bada kuɗin Cikin wannan Sati da sati mai zuwa domin zamu fara jarabawa nan da kwanaki kaɗan masu zuwa.

Wannan shine matsayar da muka cimma.

Kusani munyi iya ƙoƙarin mu domin muga mun kauce wa wannan matsaya amma abin yaci tira.

Munsan Halin da ake ciki, amma mu sani ilimin yaran mu na da Muhimmanci kuma babu wanda zai biya mu sai Allah.

Muna roƙon Allah ya Saka Muku da alheri, ya kuma baku ƙarfin gwiwan sauƙe wannan nauyi.

Sannan in akwai mai wata shawara ko wani ƙorafi zai iya tuntuɓar mu a kowani lokaci.

Allah yasa mu dace.

Wassalamu Alaikum

Nurul Huda Academy, Shendam

Email: [email protected]

Phone: 08069638767, 08034313554


Leave a Reply