Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wa barakaatuh
Sayan kayan karatu yana daga cikin abubuwa masu muhimmanci wurin taimaka wa karatun yara, da kuma ƙara musu hazaƙa. Wannan kayan karatun ya shafi
- Littafan karatu
- Littafan Rubutu
- Abin rubutu
- Jaka
Akwai abubuwa da yawo da yaro yake buƙata domin sauƙaƙa masa hanyar karatun sa amma wa’innan abubuwa da muka ambata guda huɗu sune sukafi muhimmanci.
Sama wa yaro littafai da yake buƙata kama daga littafai na rubutu da na karatu yana matuƙar taimaka wa wurin ƙara fahimta da hazaƙar yaro.
Shiyasa muke jan hankalin iyayen yara duba da cewa an kusa komawa makaranta, suyi ƙoƙari wurin ganin sun saya wa yaran su littattafa da suke buƙata.
Littafan karatu ana sayan su ne sau ɗaya a shekara, har sai sun canza aji kafin a sake saya musu wani.
Allah yasa mudace ya ƙara ƙarfafa mana guiwa.
Leave a Reply